31 parts Complete Tana shiga cikin dakin, taji an janyo hannunta anyi gefe da ita. Cikin tsananin tsoro da bugun zuciya ta daga baki zata saki ihu, taji an sanya hannu an rufe mata baki, a lokaci guda kuma aka juyata tana kallon wanda yayi mata wannan aika-aika.
Ta saki wani numfashi da bata san lokacin data rike shi ba, ta jefa mishi harara cikin wasa. Duk da cewa manyan fararen idanunta babu abinda suke fitarwa sai tsananin kauna mai tsafta.
Ya kasheta da murmushin nan nashi da har kullum yake kashe mata jiki, ya kanne mata idanu,
"Hello, love!".
*
Wai bahaushe yace 'hali zanen dutse!', 'mai hali baya canza halinsa!'.
Bahijjatu tayi tunanin wadannan duk fada ce kawai, sai da ta kwashe watanni shida bata cikin gidansu ta koma, ta ga babu abinda ya canza zani daga tsarin rayuwar gidan.
Wata irin rayuwa ce ake yi a cikin gidansu mai matukar daure kai. Rayuwar da babu girmama na gaba, babu bautar Allah, babu kuma tsoron Allah a cikinta.
Bata san cewa rayuwarta na shirin yin juyi wanda bata taba zata ko tsammani a wannan dawowar ba.
Ku biyo matashiya Bahijjatu domin jin ta yadda zata karbi wannan canji da yazo mata babu zato balle tsammani, ba kuma tare da ta shirya ba.
Wannan littafi kyauta ne, wanda zai dinga zo muku a duk lokacin da damar yin typing ta samu... :)