Soyayya ba tai min adalci ba. A lokacin da na karɓeta hannu biyu sai tai min gudun wuce sa'a. Ashe! rayuwa ba ta da tabbas! mutuwa kan zowa mutum aduk lokacin da bai za ta ba,ta yaya rayuwata za ta tafi daidai in babu mahaɗinta.Sai dai na gasgata ALLAH shine mai yin yanda ya so.
Kwatsam bayan zaman makokin da na sha na tsawon lokaci, sai gashi ta dawo min da ƙarfinta, ban ƙasa a gwiwa ba, na kuma karɓar soyayyar a karo na biyu, wadda ta zo min cikin gwagwarmayar rayuwa mai haɗe da haɗarurruka, farmaki, taskun rayuwa, bala'oi da ƙalubale kala kala kuma mabambanta.Zan iya cewa na yi dana-sani a soyayya.