5 parts Complete Kallon Umar nayi ina murmushi, "handsome, bari mu wuce ko?".
Ya gyada kai, "Ok Sweety, zamu yi waya ko?".
Na jinjina kai, "in shaa Allah. See you!".
Har ya juya ya tafi, sai kuma ya juyo da sauri, "hey, bari in miko miki fruits".
Na daga baki da niyar cewa na gode, Yaya Bilal ya katse ni ta hanyar yiwa motar key. Ya kalli Umar, "ta gode, sauri muke". Da wannan yaja motar. Ina hango Umar ta cikin gilashi yana daga kafada.
Munje main gate, na juya na kalleshi, nace "Yaya ko zaka ajiye ni anan kawai, sai in karasa ciki?".
Yadda kasan bango, haka ya maida ni, ko kallon inda nake bai yi ba. Bai ma nuna alamun yaji abinda nace ba, sai ma ya karawa motar wuta ya shige cikin makarantar.
A bakin hostel ya samu waje yayi parking din motar, na fara yunkurin bude kofar ina jera mishi godiya,
"na gode Yaya, a gaida Anty Ameerah".
Sai da na fita, ina kokarin maida kofar in rufe, naga yana miko min leda mai dauke da tambarin Bitmas, na kalleshi fuskata dauke da alamun tambaya, kafin inyi magana ya riga ni, "karbi mana, kina bata min lokaci!".
Nasa hannu biyu na karba, nace "nagode, Allah Ya amfana". Yace "Ameen" a kaikaice, yawa motarshi wuta ya kara gaba. Ni kuma na shige cikin hostel.
~Wannan littafi tsakure ne kawai. Zaku iya samun cigaban shi a zaurenmu na WhatsApp. Ga duk masu bukatar shiga, akwai bayanan yadda zaku yi ku shiga a ciki.