"Inna Hajjo don Allah karki kashe ni wallahi ba laifina bane duwatsun ne sukaƙi kamawa kuma kince kar insa makamashi, don girman Adda Aisha karki duke ni na tuba Inna bazan ƙaraba wayyo Allah" Tana maganar tare da kare duk inda Inna Hajjo take dukanta musamman kanta, Ya Umari ne ya ɗago ta haɗe da jinginata a jikinshi shima kukan yakeyi ɗago jajayen idanun shi yayi ya kalli Imam da shima idon shi duk sun rune sun canja launi, kunkuyar da kanshi yayi haɗe da cewa "Kabani izanin ramawa Inna Wuro dukan da aka mata" Cikin kuka yayi maganar "Bazan baka izini ka duki matata ba kuma ban yafe maka ba inhar kayi mata kallon banza" Imam yayi maganar cikin ƙunan rai "Lallai ya tabbata bakai bane mahaifin mu kuma naƙara yarda da maganar da matarka take faɗa muba ƴaƴan sunna bane sannan Imam bashi bane mahaifin mu"......... Turƙashi donjin waye mahaifin nasu kuma ya rayuwar su yake komawa sai kubiyo ni don jin wannan sarƙarken labarin karku manta Votind and Comments ɗinku shine farin cikina kuma ku gayyato ƴan uwa da abokanar arziki suma suji abinda labarin ya ƙunsa