Ta bude idonta ta ganta kwance cikin kurmumin daji,ta duba gabas da yamma bata kowa ba face iskan itatuwa dake kadawa Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ta fara fada,ta karanto kullakuzai sai a lokacin ta fara tuno abubuwan da suka faru ta da ita.Ta tashi jikinta duk ya mutu tana tafiya har ta kawo bakin titi,daga gani titi ne da matafiya ke wucewa.A bakin titi ta zauna ta dukar da kanta kasa tana zubar da hawayen bakin ciki.All Rights Reserved