...mahaifiyata ta 'bata tun ina da shekara takwas a duniya,... a lokacin da na dawo da sakamakon shedar kammala primary na tarar da gawar mahaifina kwance..., kawu na daya d'auki alwashin ruqo na ya guje ni a lokacin da nake tsananin buqatar sa...na tsinci kaina cikin mafarki da daddyna a kullum yana kuma jaddada min kada na bari haske na ya kufce min, lallai na kasance tare dashi..., se dai kuma na farka na ganni cikin wata rayuwa da ban ta'ba kawo wa cikin kundin littafin rayuwata ba...bayyanar Ammi na gefe guda kuma zaratan samarin biyu dake fad'i tashi a kaina, 'yan uwan juna, jini d'aya...shin ina zan kama?...