Sosai take a tsorace, ganin komai take tamkar a mafarki ji takeyi tamkar ma ace bata rayuwa a doron qasar, se zare ido takeyi tana kallon qungurmin dajin datake ciki, gata a d'aure ba hanyar guduwa, tayi iya kacin qoqarin taga ta qwace kanta amma sam abun ya faskara ya kuma tunzura, tunaninta d'aya yanzu idan wani naman daji yazo ya cinyeta ya zatayi kokuma wani mugun aljani gashi ko dankwali babu a kanta, babban tashin hankalinta shine sallar dabatayi ba, tun shekaranjiya da aka gudo da ita rabon datae sallah!!!! zata iya d'aukar kowane hukunci amma banda na hanata sallah!!! yaya zatayi da tulin sallolin dake kanta? batada halin yin koda taimamane sabida a d'aure tamau take to meye mafita?!!!!!!!