Ina hanya? Ina mafita? Ina zata bi ta ga haske a rayuwar ta? Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma abunda ta dade tana so da muradi a rayuwar ta. Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma farin cikin wanda ta fi so fiye da kowa da kuma komi a kaf fadin duniya. Koh a mafarki, Hadiza bata taba tunani irin wannan rana zai zo ba a rayuwar ta; bata taba tunanin zata sama kan ta a cikin rudun da take ciki ba sai dai kuma ta san cewar duk abunda ke faruwa a cikin rayuwar ta rubataccen lamari ne, wanda Allah ya riga ya rubuta faruwar shi tun kan ta zo duniya. Tana da tabbacin cewar da za a buda takardan Lawh-Al-Mahfouz, toh tabbas za a sama abunda ke faruwa da ita ta a cikin shafin da aka ware musamman dan rayuwar ta. Lawh-Al-Mahfouz is a story of pain Of sacrifice Of strife Of longing A story of undying love.