labarin na 'kunshe da Yaudara, Kiyayya, Soyayya, Tausayi, rikon Amana, Nishadi, Rudani, Juriya, Kaddara, Son abun duniya,.........
A takaice! littafin na kulle da sako dan nishadantar, wa'azantar da mai karatu.
In Summary........
Saifullahi (Saif) yarone, dangatan dangi, uwa uba harda sauran dangi, babu abunda yataba naima ya rasa, Saif nada ilimin arabic da boko, ladabi da biyayya dan gidan hutu da tarin dukiya saidai yanada Mahaifi Alhaji Sadiq (daddy), mai murdaddiyar ra'ayi, dan jari hujja, bin Bokaye kamar abin adone gun Daddy,......
mahaifiyar Saif Hajiya Salma(mommy), macace maison ra'ayin mijinta saidai Mommy bata yarda ta biyemai gun bokaye ba .......
shin ko Daddy da Mommy zasu amince da bukatar Saif a soyyaya!????
****************
Zinaru yarinya ce kekkyawa yar Sarkin Garin Rano,
kaddara da kiyayya sukasa tagano ita yar tsintuwace ba yar Sarki ba,
hakan yasa tazo kasar Nigeria domin naiman iyayenta.....
shin ko zata gansu raye? ko amace????????
Kalmar QADDARA kalma ce dake rataye bisa wuyan kowanne bawa,haka rayuwa ta gada,tafe take da QADDARORI kala kala,masu zaqi da akasin haka.............
SUMAYYA na kallon yadda KUNDIN QADDARARTA ke ta bude mata shafi bayan shafi na TATA QADDARAR kowanne shafi kuma da irin nasa salon karatun da yake biya mata.....
Shin wai sai ko yaushe KUNDIN ZAI QARE?
sai yaushe zata kammala bitar QADDARORINTA?
Kuyi nitso da linqaya cikin labarin don samun amsoshin kalolin qaddarar tata da kuma ranar yankewarsu
'Yar mutan HUGUMA kuma UWA GA MUHAMMADIYYA ke riqe da alqalamin jagorancin labarin..........