'Wanan kalmar! Wanan tausasawar! Wanan musayan kalmar Ta HAƘURI, da take ta kai kawo tsakanin tafiyarta zuwa mafarin ƙunsar takaicina, data gagara yi tun farko su suka zama sila na janyo mata rashin madafa acikin tafiyar da ta fara yinta, cikin taurin kan da ya zame mata sila na ƙin haƙura da tausasawar da Abdul keyi mata, da yanzu tana gidanta. Gashi ita ba'a Bauchi ba ita ba a Kano ba. Abanza kuma tazo tana haƙuri da shanyuwa atsakiyar ranar da babu girgije ko kuma gajimaren da zai tare mata sauƙaƙa jin sauƙar zafinta atsakiyar kanta.'
Wanan shine mafarin wahalar MUBARAKATU acikin tafiyar ta, wadda hanyar Bauchi ta zame mata kamar hanya mafi sarƙaƙiya da ƙunci.