'Ina kika dosa?'. Na ji wani sashi na zuciyata ya sanar da ni hakan. Sosai na ji duniyar ta sake hautsine mani, ba abin da nake tunawa sai maganar mahaifina a ranar da aka daura mani aure na zama matar Adamu. "In har kika yi sake wani abu ya fallasa akan lamarin nan, kar ki sake ki tunkaro mani gida, ki nemi wani wajan da za ki kafa rayuwarki".All Rights Reserved