Wasu hawaye taji sun zubo mata, ta fashe da kuka, kukan ta ne yasa hankalin sa ya dawo jikin sa...
Ta hau dukan kirjin sa tana wannan wane irin mugun wasa ne Ahmad, ni bana son irin wannan wasan , kai da bakin ka kace kaima kasan ina sonka...
Dukansa takeyi tana kuka....shidai yayi lamo yana saurarar ta kawai dan bai san hawa ba bare sauka...
Wannan ai ganganci ne akan me zakayi kokarin kashe kanka bayan ni kai ka hana ni kashe kaina...
Idan ban so ka ba wa zan so a duiyar nan ahmad, wa nake da shi bayan kai...
Kaima kasan na dade da kamuwa da sonka, dan allah ka tashi, AHMAD!! AHMAD!! AHMAD!!.....
Ladi tace"Bazaki taba Auren mai kudi ba sai talaka, talakan ma tukuf Wanda sai kun wahala zaku samu abinci" "yarana ne kawai zasu Auri mai kudi"
Matsiyaciya mai kama da mayya, yar tsintarciyar mage " Ba abinda Nasreen keyi banda hawaye".................
Toh! Masu karatu ku biyo ni dan karanta wannan labarin.
Shin abinda ladi ta fada zai tabbata?
Mai yasa ladi tace yaran ta ne kawai zasu auri mai kudi?
Mainene alakan ladi da Nasreen?
Toh masu karatu, ku biyo ni cikin littafin "ZUBAR HAWAYE NA" dan samun amsosin Tanbayoyin ku.
Ku biyo alkalamin Gimbiya Ayshu 📝📝📝.