ABINDA KAKE SO
  • Reads 82,621
  • Votes 7,083
  • Parts 72
  • Reads 82,621
  • Votes 7,083
  • Parts 72
Complete, First published Feb 17, 2019
Mature
Cike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka raina. Ba ki min adalci ba ba kuma kiwa kanki ba" ita kam kuka ta ke wiwi da kyar ta ke iya magana "Kayi hakuri Ya Mukhtar ba zan iya ba"...

 Kallon tara saura kauta ya ke binta dashi kafin yace " kinji kunya Suhaila, kinyi asarar rayuwa in dai wannan rayuwan ta marasa tarbiyya kika zabawa kanki" ba tare da ta kalle shi ba ta tabe baki tace "Da kake maganan tarbiyya ai da sai kaje ka tuhumi Mahaifiyarka domin ko komai kaga ina yi tarbiyya..." Bai bari ta karasa ya kifa mata mari. A zabure ta dago idanuwanta tana shirin ramawa sai dai ido hudun da suka yi yasa ta yi kwafa ta wuce daki hade da jan tsaki.

 Zaune ta ke kan kujera a zahiri tana kallon yaran da ke gaban ta suna homework sai dai gabadaya hankalin ta bai kansu. A haka mahaifin yaran ya fito daga daki ya iske su "Ah ah Fadila ya kika kyale su su kadai suna Homework in ai da kin jawo su kunyi tare koh" kerere ta kalle shi sannan ta tashi a fusace ta yi daki ba tare da ta tsaya sauraren Abinda ya ke fada mata ba. Direct kan Gado ta nufa tana fidda wani hawaye mai zafi. Shin wannan wani irin rayuwa ce? Ta rasa wani irin zama ta ke a gidan Najib. Ita dai kam ta gaji dole ta nemi mafita.

 Kanta a sunkuye har ta gama sauraron mahaifinta. Kaman ance ta dago su kayi ido hudu da Faisal yana shigowa falon nan take idea ya fado mata da sauri tace "Yauwa Ya Faisal kazo a daidai" bai gane mai ta ke nufi ba har yazo ya zauna kaman yanda aka umurce shi. Cikin dakewa ta ce "Yauwa Abbah daman Ya Faisal ne kadai mu ka daidai ta dashi yace zai zo ya same ka kuyi magana yau" siririn murmushi Faisal ya saki gane idan zancen ta ya nufa. Lallai yarinyar nan dole ya koya mata hankali "Hakane Abbah daman munyi da ita yau zan same ka" murmushi mahaifin nata ya saki cike da farin ciki...
All Rights Reserved
Table of contents
Sign up to add ABINDA KAKE SO to your library and receive updates
or
Content Guidelines
You may also like
KHADIJATUU by KhadeejaCandy
62 parts Complete Mature
NOT EDITED ⚠️ Yayi kyau matuƙa, yadin ya fito da farinsa da kuma kyaun fuskarsa, Idan ka kalleshi, sai ka ganshi kamar mai cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali, al-halin sune abubuwan da suka masa tawaye. A hankali ya sauke ajiyar zuciya yana lasa lip ɗinsa. Juyowa yayi yana wani taku da idan baka karance shi ba, zaka iya cewa na wulaƙanci ne da nuna isa, al-halin babu hakan a tare da shi ko kaɗan, ƙarasowa yayi gun da Khadijatu take kwance ya duƙo daidai ita, ya hura mata iska a fuska kamin ya kai hannu ya taɓa jikinta. Hannun yasa ya tallafota ta dawo saman cinyoyinsa, fuskarta na fuskantar tasa, ido ya sakar mata kamar yau ya fara ganinta, a hankali ya kai hannun ya shafa gefen fuskarta, tausayinta ne yake ƙara shiga zuciyarsa. Shi kansa yana ji a jikinsa akwai wani sirri dake tsakaninsa da haɗuwarsa da Khadijatu, sirrin da har yanzu bai san na minene ba, yana jin shi ɗin wani bangone a shafin rayuwarta, lallai idan har babu shi a ƙaddarar Khadijatu toh babu wanzuwar labarinsa a doron ƙasa, yana ji a jiki da kuma ruhinsa domin ita akayi shi, kamar yadda yake jin da a'ace ya rabu da ita tsakanin jiya zuwa yau da bai san yadda rayuwarsa zata kasance ba, bai san wane irin hali zai samu kansa ba, dan baya taɓa rasa natsuwarsa idan yana kusa da ita, idan tayi nisa dashi ji yake kamar ya rasa wani ɓangare na jikinsa. Ba sonta yake ba, dan baya tunanin zai iya buɗewa wata ƴa mace zuciyarsa, tun bayan abunda Malak tayi masa, sai dai kuma yana jin fiye da yadda yake ji idan yana tare da Malak, yana jinsa cikin wani yanayi wanda bai taɓa ji ba idan yana tare da Malak. ® 2018
DUNIYA BIYU!!!  by jeeedorhh
12 parts Complete
Gefen wasu samari uku da suke ta faman tada hayaki kamar tashin duniya ta rakube, ta mikawa Bangis -mai shagon- kudin hannunta. Tace, "magi mai tauraro zaka bani na talatin da aji-no-moto na ashirin". Ya zuba mata a leda fara ya mika mata. Ta juya, wani daga cikin matasan ya fesar da hayakin daya busa, ya sauka akan fuskarta. Ta sanya hannu tana kore hayakin, tana tarin daya sarketa sakamakon shakar tabar da tayi har cikin makoshinta. Ta bude idanunta dake mata zafi, babu mamaki ma sunyi ja, ta saukesu akan wanda ya aikata mata wannan ta'addanci. Babu abinda ya dauki hankalinta a tattare dashi sai idanunshi, irin idanun dake nuna wuya da tsananin duhun rayuwa da suka gani, suka kuma jure. Duk rashin kunyar mutum, karya yake yace zai tsaga tsakiyar idanun mutumin nan yace zai mishi rashin kunya. Don haka ne yasa ta kame bakinta, 'yar Allah Ya isa din data dauko daga cikinta zata yi, ta tsaya a makoshinta. Ta sadda kai ta kara rabawa ta gefensu ta wuce. Bata sani ba, wani abu game da wannan bakon mutumi da bata taba gani ba, seems nagging. Ta kasa fitar dashi daga cikin ranta. Dai-dai zata karya kwana, ta juya tana kara kallon tiredar. Yanzu ya fito daga cikin tiredar, yana tsaye daga waje. Sai dai kaifafan idanuwan nan nashi suna kanta kyam. Wata irin kunya da faduwar gaba suka rufeta, musamman dan guntun murmushin da taga yana yi mata. Tayi saurin yin kasa da kanta, wani dan karamin murmushi itama yana ziyartar bakinta, kafin ta juya da sauri ta karya kwanar.
You may also like
Slide 1 of 10
KHADIJATUU cover
WADATA cover
GIDANMU(OUR HOUSE) cover
MATSALARMU A YAU!  cover
Luigi's Empire (Complete) cover
JIRWAYE✔ cover
BABBAN GORO cover
DUNIYA BIYU!!!  cover
ဇာတ်လိုက်မရဲ့ သိမ်မွေ့နူးညံ့တဲ့ သူငယ်ချင်းလေး။ cover
KANA NAKA..! cover

KHADIJATUU