SARTSE ba a iya tafiya kawai ake yinsa ba, wani Sartsen yakan zo acikin daƙushewa da kuma kankare mana burika da hasashen mu. Idan muka kalli rayuwa afai-fan hannun mu zamu ga wasu abubuwan dalili kawai suke buƙata dan wargaza ka da kuma tanadin da kayima rayuwar ka. Bai zama cikin jerin mazaje masu ji da ƙumajin ƙwanjin su ba, bai kuma zama cikin wanda suke ware kansu da zama fiye da ko wani namiji agarin ba. Hakan sai ya zama mashimfiɗi na aika masa wargi agare shi, aka kuma aika ko wata tsana da kyara agare shi. Ciki kuwa harda wargaza Aurensa da ake shirin ɗaurawa. Wanan sai ya kawo sauyi acikin rayuwa da duniyar MA'ARUF.All Rights Reserved