12 parts Complete Tunda Anty ta fara magana, Prof yake kallon ta, idan ka kalle shi ba zaka taba fahimtar a yanayin da yake ciki ba, ba zaka fahimci emotions din shi ba, Amma yadda yake kallon Anty, da yadda ya bata dukkan hankalin shi, Abu ne da zai tabbatar maka cewar maganar babba ce. Anty ta gama bayanin ta tsaf sannan tayi shiru tana jiran ganin hukuncin da Prof zai yanke. Cikin nutsuwa yace
" A Ina ta samu?"
Shi ne tambayar da yayi ma Anty, maimakon tayi masa bayani se cewa tayi
" Ai na Gama nawa professor, abin da ya rage kaji ta bakin HAIRAN kawai!"
"Me yasa Anty?"
Cike da nutsuwa tace
" Saboda zaka ga kamar kare ta nake, Amma idan tayi maka bayani Ina Jin zaka fi gamsuwa da kyau!"
Daga haka Prof yayi shiru Yana son ya auna nauyin Abubuwan da Anty ta fada Masa, se kawai ya Mike yayi ma Anty sallama ya fita. Kunsan yadda tsumma yake idan aka tsoma shi cikin ruwa ko? To haka Prof yayi, gaba daya jikin shi ya saki, yayi shiru tamkar wani kurma, ya bude mota ya shiga ya kifa Kan shi akan steerer wheel, shi yasa take fada Masa lallai lallai se sun rabu kenan? To Ina ta samu shi ne tambayar da take zuwa Masa...
***
Shigowa ta kenan daga lecture, na gaji, gajiya kuwa matuka saboda shirin exams da muke, har lokacin bana cikin dadin rai, Abu ya kusa wata daya Amma still nukurkusa ta yake Yi. Ina Zama Saman gado Ina kallon Nuriyya da ta dakko wani gari tana kokarin kwaba shi da ruwa nace
" Me zakiyi?"
Tace
"Kunun aya Mana!"
Se nace
" Kunun Aya Kuma, gaskiya Kin iya bawa Kai wahalar, ana shirin exams din!"
Tayi dariya tare da daga min wata transparent ziplock tace
" Waye zai Baki wani wahala, wannan ai is outdated, halan Baki San Islah foods ba ko? To ita take siyarda wannan garin na kunun Aya, yours is just to make little effort se ki Sha!"
Nayi murmushi Amma kafin nayi magana se Naga Kiran Anty na shigowa cikin waya ta, da sauri nayi excusing Kai na sannan na mike Dan fita