19 parts Ongoing Me Nauyin baki ke janyowa?
Me Nauyin baki ke haifarwa?
Me ke afkuwa da mutum sanadin nauyin baki?
ABUBAKAR SADEEQ ya tsinci kanshi tsumdum cikin matsananciyar soyayyar HALIMATU SADIYA tun bata san kanta ba har ta kai ga ta mallaki hankalin kanta, amma NAUYIN BAKI ya hana shi furta mata har ya kai matakin ƙarshe na rasata, wanda a wannan lokacin bayyana mata soyayyarsa ba lallai ta amfanar da shi da komai ba, domin a nata ɓangaren kallon Yaya na cikin umma guda take masa, dan soyayyarta take sha da masoyin ranta kuma muradin zuciyarta ALIYU HAIDAR, wanda tsabar ƙauna da soyayya har ta kai ga sun haɗa sunansu ya koma guda, ire-iren yanda masoya ke yi AL-SAD(Aliyu+Sadiya), a haka har ta kai ga sun haura matakalar da za ta kai su ga cin ribar soyayya, ta hanyan mallakan junansu, ɗauki da shirin aurensu suke cikin matuƙar yunwar mallakan juna, sai dai wani hargitsi ya gifta suna gaf da cimma burin nasu.
SHIN BURINSU NA MALLAKAN JUNA ZAI CIKA?
SHIN WANDA SANADIN NAUYIN BAKI HAR YA KAI MATAKIN ƘARSHE NA RASATA YA MAKOMARSA TAKE?
A MATAKIN ƘARSHEN NAN ZAI IYA SAMUN WATA ƳAR ƘOFA TA MAFITA? (ONE CHANCE)?
KOKO DAI DOLE ZAI YI HAƘURI?
IDAN YA SAMU ƳAR ƘOFA SHI WANDA TAKE SO YAKE SONTA YA ZAI YI?
ANYA ZA TA BI WANDA KE SONTA TA BAR WANDA TAKE SO?
WA KUKE TUNANIN ZA TA ZAƁA KO KO WA YA KAMATA TA ZAƁA?
SADEEQ KO HAIDAR?
KO DAI DUK RASATA ZA SUYI?
AUREN WANDA TAKE SO KO AUREN WANDA KE SONTA?
Akwai wani hanzari ba gudu ba habibties, rayuwa gaba ɗaya tana tattarene kuma tana tafiya bisa doron ƙaddaran da Rabbi ya ƙaddara mana tun fil'azal, ko ya bawa ya kai ga shirinsa to ba ya taɓa iya gujewa ƙaddararsa.
MENENE ƘADDARAR SADIYA?
WAYE ƘADDARAN SADIYA?
WAI YAYA NE KAM HABIBTIES?