34 parts Complete Mature(MARRIED TO MY BEST FRIEND FATHER)
...A hankali na nisa na ƙarasa kusa da ita na zauna,ina kallon frame ɗinmu dake ajiye saman bedside drawer nace "wai me kika ɗauki kanki?" Tace "yanda kika ɗauki kanki nima haka ne" da sauri na juya na kalleta,lokaci ɗaya na ɗauke kaina ina taɓe baki nace "ni yanzu idan na amsa nace miki zan iya kallon Daddy matsayin miji wallahi na yi miki ƙarya" tace "ko saboda me?" Nace "saboda shi ya raine ni,can't u think me mutane za suce idan haka ya faru? Cewa fa za ayi.." Widad tace "kin auri mahaifin ƙawarki?" Da sauri na gyaɗa mata kaina nace "sure! Kuma ko bayan haka ai kin ga abun bai tsari ba,tunda shi ya raine ni tun ina yarinya,dan Allah kawai sai na auresa kuma? Shi fa Daddy ne" murmushi Widad tayi tace "tou dan shi Daddy ne sai me? Ai dai naga babu haramci dan kin auresa" cikin sauri nace "ehh! Na san ba haramci amma.." Widad tayi saurin katse ni tace "tou tunda kin san haka why baza ki amince ba,kinga duk abunda mutane za su faɗa sai suyi with evidence,kin san dai shi mutum ba'a iya masa" nace "ni fa Widad kin kasa fahimta ta" tace "kuma wallahi bazan fahimce ki ba,muddin baki yarda da abunda nazo da shi ba.."
Ƙaƙa-ƙara ƙaƙa! Kou yaya za'ayi wannan rayuwar auren tsakanin ƴar riƙo da mahaifin ƙawarta? Shin za ta amince ne ko a'a? To find out how the story will turned out,just follow this fairy tale of love and romance.