Farida ce ke tsula gudu a mota hawaye ya wanke mata fuska jikinta yana rawa ta kira number Nura, bugu d'aya ya d'auka ta tari numfashinsa da sauri
"Nura, Nura wallahi bai mutu ba yana nan a raye, yanzu na ganshi a Asibitin Mahaukata na nan cikin Abuja, na shiga uku naaa"
"Ke ki natsu kimin bayani waye kika bani ne haka duk kika wani firgice?"
"Imran, Imrann na gani yanzu a Asibitin Mahaukata, Fadeela k'awata itace ke kula dashi"
"What? Imran kuma? Badai Imran ba domin akan idona suka birne gawarsa..."