labarin wata yarinya ce bafulata wacce ta fito daga ta fito birni domin karatu, ta samu ta shiga jami'a domin cika burin ta na karanta noma da kiwo domin ta dawo ta taimakawa rugarta wanda shanaye da mutane suke mutuwa sanadin ciwon da ba su sani ba. gonakin su kan su suna bukatar ilimin zamani domin bukasa su.
sai dai akan hanyar ta ta cimma mafarkin ta ta gamu ta iftila'i, ta yaya zata koma gida ta sanar da su ciki da bata san uban shi ba? mai zai faru da karatun ta, da wanne ido zata kalli iyayen ta da 'yan rugar su wanda suka yarda da tarbiyyar ta har suka amince da ta zo ta fitar da su daga kuncin rayuwar da suke ciki.
Duk rudu da ta shiga akwai mutum daya da san amsar tambayoyin ta, sai dai ba zata fada mata ba domin akwai biyan bashi gaba a tsakanin su.
ku biyo ni a cikin littafin don jin koma meye
Taku.
Zainab s. zarewa
(Zeezee- zarewa(Mrs. Abdul)).