"Ruqayyah yaushe kika fara tumbi ke da ko me kika ci cikin ki baya tab'a dagawa?"
Baki Ruqayyah ta bud'e tana dariya take fad'in "wallahi ummah na fara tumbi,ba ki ga har k'iba na k'araba?"
"Abunda na gani kenan shi yasa nake tambayarki"
"Uhmmmm! Ummah kenan wallahi babu komai,murmushi Ummah tayi lokacin da Ruqayyah ke fita da plate d'in da sukaci abinci,amma hankalinta bai kwantaba saboda wani tunani da tayi lokaci guda ta kwallawa Ruqayyah kira
"Ummah ga ni!"
"Zauna magana za mu yi" guri ta samu ta zauna,"kin san me nake so dake?" Kai ta girgiza alamun A'a,ummah tace "so nake ki fad'amin yaushe ne rabon ki da ganin bak'on ki?"
"Wane bak'o kuma ummah?"
"Al'adarki nake tambaya!"
#Turk'ashi! Masu karatu ku biyo ni cikin wannan labari don jin yadda aka haihu a ragaya!