YARDA DA KAI (Compltd✔)
  • Reads 80,307
  • Votes 2,340
  • Parts 12
  • Time 2h 39m
  • Reads 80,307
  • Votes 2,340
  • Parts 12
  • Time 2h 39m
Complete, First published May 25, 2019
ldan YARDAR KA tayi yawa akan mutane, to kamar ka basu lasisin kwaye maka baya ne.
 Awanan duniyar tamu da son kai yayi yawa, cin amana ta zama ruwan dare, ka yarda da mutum yaci amanar ka, ɗan uwa ya tsani ɗan uwan sa saboda wata ɗaukaka ta duniya. Wanan shi ne ga janyo ƙin yarda da kowa arayuwar AHMAD NASIR, zuciyar sa ta bushe da ƙiyayyar mutane, ayayin da gefe guda yake tsoron mu'amala ta haɗasu da ko wani mutum ciki kuwa harda ƴan uwan sa.

 LABARIN YADDA DA KAI yana magana akan yanda zamani yayi hautsinewar mugunyar ɓarna, sakaci da al'amura suka ƙarama mai rauni raunika acikin zuciya.
All Rights Reserved
Sign up to add YARDA DA KAI (Compltd✔) to your library and receive updates
or
#24soyayya
Content Guidelines
You may also like
FATU A BIRNI (Complete) by suwaibamuhammad36
18 parts Complete
"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata abunda ba'a tsammani domin ya cika wannan alƙawari da ya ɗaukawar mahaifiyarshi, aka yi dace ya gano inda take. Wani abun takaici shine a maimakon ya samu ƴar'uwar Maminshi kamar yanda ya ci buri, sai ya haɗu da ƴarta kwalli ɗaya tak da ta haifa a duniya ta bari cikin ƙauyanci da kuma rashin wayewa. Baƙin cikinshi bai tsaya a nan ba, domin dattijon da yake riƙe da ita a take ya aura masa yarinyar ba tare da ya iya kaucewa wannan mummunan ƙaddaran ba. Ya tafi ya barta ba tare da ya sake waiwayarta ba, ya kuma tafi da wani kaso na zuciyarta ba tare da ya sani ba. Fatu (Fatima) ta ji haushi, sannan tana cikin baƙin cikin tafiyar da mijinta yayi ya barta. Tun tana tsumayinshi tana fatan ya dawo ya ɗauketa, har zuciyarta ta daskare da tsantsar tsanarshi na wofintar da ita da yayi, da kuma banzatar da igiyar aurensa dake kanta. Tayi alƙawarin ɗaukan fansa, ta kuma yi alƙawarin raba tsakaninsu ko da duniya zasu taru su hanata. Sai ta nemo shi a duk inda yake. Ta shiga cikin Birni nemansa, a nan kuma ƙaddara ya gifta tsakaninsu suka haɗu a lokaci da kuma yanayin da basu yi tsammani ba. Shi kuma ganin kyakkyawar baƙuwar fuska mai ɗauke da kamala, ya sashi faɗawa cikin sonta dumu-dumu ba tare da ya shiryawa hakan ba, kuma ba tare da ya gane cewa Matarsa ce ta Sunnah ba, Halal ɗinsa. Me zai faru idan Fatu ta haɗu da mutumin da ta ƙullata tsawon shekaru a yayin da shi kuma yake jinta a zuciyarsa tamkar ruhinsa? Me kuma zai faru Idan wasu sirrikan suka bayyana a lokacin da ba'a shirya musu ba? Fatu mace ce ɗaya mai hali mabanbanta; Fatu- Matar Sultan. Fatima- Budurwar Sultan.
You may also like
Slide 1 of 9
FATU A BIRNI (Complete) cover
'Ya Mace (Completed)✅ cover
ZAN SOKA A HAKA cover
MATAR SHEIKH cover
MIJINA NE! ✅  cover
Her Boyfriend, My Husband cover
BA KYAU BA ✔️ cover
ZAFIN RABO ✔️ cover
INDO SARƘA COMPLETE cover

FATU A BIRNI (Complete)