Mikewa Barrah tayi, yanayin jikinta ya nuna sanyi da kalaman Mu'azzatu, sosai take tausayin ta sosai take jin rashin dadi game da yadda take ganinta a ciki, zuciyarta na zafi sosai da sosai, amma hakan ba yana nufin zata bata shawarar kashe auren ta bane, ba za ta taba yin wannan kuskuren ba, ta tabbata ita kanta sai ta san tayi kuskure mafi girma a rayuwarta.
"Shi..kenan Barrah sosai nagode miki, kulawa da kike yi mani, ba kowa bane zai iya yi mani...".
Ta faɗi. tana mikewa cikin rawar murya, kamar za ta rushe da kuka.