Motar ta tarwatse, k'arfin shigowar gingimarin dake d'auke da itace ya haddasa wata k'ara kamar ta tashin bam, k'ofofin motar suka yage daga jikin bodin, gaba wajen zaman direba ya fita ta taga, injin motar ma yayi tsalle wani wajen. Ka'ra mai yawa ta cika iska, yadda k'arfe ke had'uwa da d'an uwansa, yadda k'arfe ke datsa bishiyoyin gefen titin da kuma yadda k'arfe ke k'onewa. Daga wannan lokacin, duk abinda FADEELAH MALIK tayi ya faru ne bayan BINTUN IKARA ta mutu, kuma dole ne FADEELAH ta fuskanci dukkan laifin da BINTU tayi! **** Ya kai hannu bayan wuyansa ya shiga murza fatar wajen a hankali, har yau yana iya tuna yadda fuskarta take a lokacin daya fara ganinta, nad'e cikin mayafin dake nuna shaidar addininta, sannan kamar kullum idanunta na manne da siraran glass d'in da ya k'ara fito da ilhamarta, idanunta kyawawa masu maik'o da kyalli, suna haskawa kamar an kunna wuta ta k'asansu. Sai dai mafi rincab'ewar al'amarin tana masa kallon tsana ne! tsana wadda ke tasowa tun daga k'asan zuciyarta, tsana wadda baya tunanin wani mahaluki ya tab'a yiwa waninsa, sannan tsana irin wadda bai san dalilin wanzuwarta ba. Abinda kawai ya sani a yanzu shine da FADEELAH da BINTU abu d'aya ne, zuciya d'aya suke rabawa don haka in har ta tsane shi a matsayin FADEELAH MALIK, yanzu da ya same ta a BINTUN IKARA ma babu abinda zai canja!All Rights Reserved
1 part