13 parts Ongoing Aurenta da Khalil kaddara ne. Zuwanta gidansu a matsayin mai aiki jarabta ne. Zama gidanshi tare da matarshi kuma bala'i ne. Da wanne zataji? Miji wanda ya tsaneta tamkar mutuwarsa ko kuwa matarsa da bata da burin daya wuce ta tozartata dukda kuwa batasan itadin matarsa bace? Ko kuwa karyata musulunci da kowa yakeyi?
Tabbas, K'abila...itama musulma ce. Amma a rayuwar Fatima Batul, hakan abu ne mai wuyar bayyanawa.
Kyara, tsangwama da wulakanci sune abubuwan da tafi sabawa dasu a duniya har tana ganin bazata tabi jin dadi ba a rayuwarta. Kasantuwar mahaifiyarta Igbo, tunda Batul ta bude ido babu abunda ta sani face kunci da bakin ciki sai tarin hawaye. Wai dama shi musulunci idan ba a ciki aka haifeka ba Allah baya amsarka ne?
Ko kuwa dai dole sai kai bahaushe ne ko bafulatani sannan musuluncinka yake zama ingantacce? Ana kiranta K'abila, ko kuma ace mata Tubabba, kai harma muna musulma ana kiranta wai duk dan kasancewar mahaifiyarta inyamura duk kuwa da cewar ta musulunta daga baya.
Batul bata gara jefa kanta cikin ukuba ba sai bayan aurenta da Khalil, ga bala'in mahaifiyarsa da yan'uwansa, dangi da abokansa...shin ina zata saka rayuwarta ne?Data sani da bata gudu tabar gida ba, data tsaya dangin mahaifinta sunyi duk yanda sukeso da ita, da bata roki alfarma ta auri Khalil ba...
---
Labari ne mai cike da darussa daban daban akan addini, al'ada, zamantawa da kuma tsantsar soyayya. Ku biyoni dan ganin yanda labarin Fatima Batul da angonta Ibrahim Khalil zai kasance...