D'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba ta k'ara shiga tsananin tashin hankali, idonta kamar zasu yo k'asa ta dafe kanta tace
"Na shiga ukuna ni Jannat"
Sai ta saki wani gigitaccen k'ara.
Abbanta ne kwance a tsakar d'akinta cikin jini, wanda ya malale tiles d'in d'akin, ya dafe gefen cikinsa da hannun damansa babu alaman rai a tattare dashi, wuk'ar dake hannunta ta kalla wanda duk jini ya gama b'ata shi tare da hannunta na hagu, kamar an tsikareta ta jefar da wuk'an a k'asa da k'arfi, wani ihun ta kuma saki wanda duk sai da ya tada duk Mutanen dake cikin gidan.