49 parts Complete d'an tsokacin labarin CAPTAIN SADIQ ya kunshi rayuwar soja ne mai zafin zuciya, d'aurewa rashin fara'a tun bayan lokacin da Allah yayiwa matarsa rasuwa, bayan ta haifa masa baby girl wadda taci suna mahaifiyarsa wacce Allah ya d'aura masa son ta, Hakan yasa duk mai aikin da aka kawo domin kula da yar tasa sukan gudu ko ya koresu, saboda rashin gamsuwa da aikin nasu, ko saboda cin kashin da suke fuskanta a wajan sa, hakan duk yanada nasaba ne da tun bayan rasuwar matarsa KAUSAR ya rasa walwala, har mahaifiyar sa ta fara gajiya da irin halin nasa, kwatsam sai ga Allah yasa mahaifiyar sa ta samo mai aiki FATUHA wadda ta adabi mutanan kauyan su da rashin jinta, haka yasa k'anwar mahaifita tahowa da ita birni aikatau gidan su CAPTAIN, ko mutanan kauyan sun huta da halin ta, ya kuke tunanni masu karatu? shin FATUHA zata d'au wulak'ancin CAPTAIN SADIQ koka zata rama tunda dama bata ji ko a kauyan su RANO mu kaftan💃