Duk abin da mutum zai zama a duniya sai ya bi ta wasu matakala wanda ke manne a jikin tsani, tsanin kan iya zama na katako wanda ruwa da rana ke saurin lalatasu wani tsanin kuma na karfe ne da sai dai yayi Tsa-tsa.
Ana samun tsani na azurfa ko lu'ulu'u ko ma zinari wanda hakan bai isa a ki kiran sa da tsani ba, hakan bai ki a bar shi yashe cikin ruwa da rana ba, hakan bai isa a daraja sama fiye da shi ba duk da kuwa in babu shi ba za a isa ga saman ba.
Maluma su ne TSANINMU. Duk abin da gobe zai haifar mana dole sai ta sanadinsu.
Ku biyo ni mu shiga rayuwar TSANI malam Muhyideen Jibril.