Kamar kowani matashi ko matashiya, Hibbatullah ta tsinci kan ta a cikin yanayin rayuwa inda ta ke son ta yi wa ubangijin ta biyayya, ta faranta wa iyayen rai, sannan ta faranta wa kan ta ita ma.
Ta hadu da ibtila'i kala kala na rayuwa wanda ya zama ruwan dare a rayuwar matasa a yau, wanda hakan ya yi sanadiyyar gurbata mutuncin ta da kimar ta a idanun ƴan uwan ta.
Ku biyo ni a kan wannan tafiyar ta rayuwar Hibbatullah mai ɗauke da ɗimbin darussa ga iyaye, malamai da kuma matasa..