27 parts Complete Ashe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka?
Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta haukace ne? Aa, kila kuma kuncin da rayuwarta take ciki shine take ganin mutanen daya kamata ace tana tare dasu?
Amma tabbas mijinta ne, shine. Ta tabbata shi din ne. Ga murmushin shi nan, dariyar shi, yanayin yadda yake tafiya. Wallahi shine!
Shin mijin nata ne ko kuwa? Da gaske shi din take gani ko kuwa? Amma ba'a mutuwa a dawo. Saidai a yanayin yanda rayuwarta take juyata, takan iya cewa ita a nata fannin rayuwar, kila mutum yakan mutu sai ya dawo.
Mijinta ne, kome zasuce bazata taba yarda dasu ba.
Aisha Malumfashi.