Sunan littafin SILAR KAFAR SADARWA lbr ne da yake mgn akn yadda ake amfani da social media na illolin sa da amfanin sa, duba yadda yanzu komai jama'a sai sun yi posting a media sabon gida, mota, aure, lbrn dai na wata ce da ta faɗa tarkon wani namiji sanadiyyar saka photunan ta a DP DA STATUS, har ya keta mata haddi, shi kuma wannan Guy yana amfani da sunan Mata ne yana kasancewa a group na mata a WhatsApp to a haka yarinyar ta haɗu da shi suna abota a tunanin ta da Mace take abota a haka har suka haɗu ya cimma burin sa a kanta ni dai manufar lbr na shine ayi takatsantsan da social media kuma jama'a su daina faɗan progress nasu a media ba kowa bane yake son Mutum da alheri, kamar ni a zama na ta Mace sai kaga mata a group suna bayyanar da sirrin gidan auren su a group ko me mazajen su suka yi musu sai sun faɗa, to ire-iren Wannan abubuwan ne ya ja hankali na nayi rubutu.