• _*Makunnin Sha'awar 'Ya mace:*_ • _Matakin farko da Uwargida za ta bi don budo sha'awarta shi ne, ta fara yin zurfaffen tunani game da ita kanta, yanayin ta da yanayin halayen ta da yanayin shau'ukan cikin zuciyar ta. Ta yi kokari ta fahimci mene ne yake danne mata sha'awar ta? In da hali ta samu littafi ta rubuta dukkanin dalilin da take ganin su ne ka iya rufe mata makunnin sha'awar ta, da kuma abin da take ganin zai kawar da su har sha'awar ta ta bude. Na sha fada a cikin wannan fili cewa, ita 'ya mace dole sai tana cikin jin dadi da kwanciyar hankali da natsuwa daidai gwargwado sun saukar mata a zuciya kafin makunnin sha'awar ta ya iya kunnuwa.All Rights Reserved