"RASHIN UBA! Itace kalmar da ke cinye zuciya da kuma daƙusar da karsashin ko wani yaro!
Fatan ko wani UBA shine kafa ma yaransa kyawawan tarihi da bar musu gobe mai kyau. Sai dai mu kam namu UBAN kallon matacce muke masa, da babu amfanin wanzuwarsa a tare da mu.
Shin dama maraici ba sai an mutu ake yinsa ba? Na yi fatan ace mutuwa ce ta shuɗe labarin mahaifinmu, ba mu ne labarin ya duƙun-ƙune ya cutar damu akan sakacin Uba ba.
Da mamaki ace yara na fatan mutuwar UBAN SU! Amma idan zamani yayi rakiya babu abin da ba zai iya sauyawa ba. Ciki kuwa harda RASHIN UBAN da bai zama gawa ba.
Sunana MAIRO kuma wannan shine labari nah!"