10 parts Ongoing Allah ya halatta aure ga kowanne dan adam mai lafiya, suma ZABIYU (ALBINOS) 'yan adam ne kamar kowa amma meyasa ake kyamatar su musamman ta fuskar auratayya? Da gaske ana gadon ALBINISM a cikin jini amma akwai wadanda halittar Allah ce ta samar da su a haka kamar HANSNA'U. Hasna'u kykkyawa ce amma ZABIYA ce....shin ko wannan nakasa itace karshen rayuwar ta? Kuma nakasar da zata hana ta zaman aure a rayuwar duniya? Shin MIJI ko MAHAIFIYAR SA ko al'ummar dake zagaye da ita wanene babban kalubalen Hasna'u a rayuwa? ni dai TAKORI na ce HASNA'U mutum ce kamar kowa ban sani ba ko kema kin amince da hakan? Mu biyo HASNA 'YAR NAJERIYA don jin walagigin rayuwar data samu kanta cikin lalurar ALBINISM.