"Ga wannan sunanshi 'Dan aike' domin ko in ya je dawowa ya ke, an hadashi ne da majinar damisa mai mura,jelar'beran da bai taba satar daddawa ba,da kuma hakorin muzuru mai kimanin kwana cassa'in, ya yarda ke tun bai san miye yarda ba,a coffee za ki 'diga, 'digo biyu ina jaddadawa!!!, ki bawa Anisa ita zata hada ta kai masa, ba so ba ko zuciyarshi ce a jikanta ba zai aure ta ba, Anisa zai aura,amma duk ranar da Najma ta furta mai da kanta tana son shi ki Kuka da kanki don babu Ruwan Boka Mugu" Ya fada yana zare idonshi da ya sha farin kwalli.
***
Gishiri ya ji a bakinshi mai hade da ruwa, lokacin ne ya gane ba ita take bu'katar handkerchief din da ya bata ba shi ke bukata, yaushe rabon da ya yi kuka? Tun ranar da ta yi wani ciwon ciki mai cike da azaba, ya bawa kanshi amsa yana goge majinar da ta samu damar zubo masa, zuciyar sa ce ta kuma tarwatsewa a karo na ba adadi jin kalaman da ke fitowa daga bakinta dukda cewa a wurinshi sun fi kama da aman wuta mai zafi, so yake ya ce mata 'I love you ' kalmomin da tun bata fahimtar magana yake fada mata saidai yau ya kasa,wani abu mai kama da Zuma rock ya danne masa harshensa da zuciyarshi kuma sai bitarsu yake kamar almajiri ya rike allonsa. Dumm zuciyarshi ta buga a karo na uku tun bayan da ta fara magana,bakin shi ya bude wanda ya yi sanadiyyar zubowar yawun da bai san da shi ba a yayinda ya cigaba da kallonta kamar wanda ya ga Tinkiya da'Ture ka ga tsiya' daurin yan mata masu ji da kansu.
***
"Haba Yayana 'dan baki!Ya kake so in yi da rayuwata ne?Na san ba Anisa kake so ba ni kake so ba sai ka fada min ba wallahi na sani, amma ka ki ka nemi aurena tun tuni? Mai kake jira? Hmmm, Ya Mir me ya sa ka canza min gaba daya? na yi ta kokarin in jure na kasa saboda zuciyata ba zata iya ba,Nisanta kanka da kake yi da ni 'kara tarwatsa min zuciya yake, Ka yi sake har Abbu ya hada aurena da Ya Jamil,gobe za a daura tunda haka ka zaba you have 24 freaking hours to decide, abinda na sani shi ne I LOVE YOU WALLAHI DA GASKE..."