ne na izzar sarauta, ta shafi kumalabari rayuwar convert da suke musulunta mu musulmai Muke Gaza tallafa musu su rayu cikin musulunce, muke hanasu inuwa, idan mun basu inuwar kuma toh fa semu tsangwamesu mu gorata musu, mu damesu da kyara, darasussukan da suke cikin wanan labari darussane da kowane musulmi yakamata ya daukesu, gudunmawace ga dukkan Wanda suka musulunta ko suka fuskanci rayuwar haka, sanan wanan labari Zan iya cewa bai shafi kowaba Dana sani, wata baiwar Allah ce ta kawomin shi, wacce Bata damuba da in fidda sunanta ko boye ba, Bata damu danayi Kari ko nayi ragi ba cikin LABARIN ansamu dacewar rayuwarta sak da littafina na tambari Wanda saboda wasu dalilai masu karfi ya tsaya, shine taso na maye gurbinsa da nata labarin dn sunyi kamanceceniya, Ina godiya GAREKI MARY ANN RAHMATULLAH, Allah ya dawwamar dake Akan addinin islama, ya Kara Miki juriya ya dubi SADAUKARWARKI.