Yunwa da ƙishirwar da suka addabe ni ne suka sanya ni kasa bacci ina yi ina farkawa sbd yunwa ta riga da tayi min illah, haka ma innata baccin kawai take yi amma na fahimci ita ma tana jin irin radadin da nake ji, don na lura sosai tunda ta kwanta take juyi.
Agogon da ke manne a dakin mu na duba ƙarfe goma dai-dai na dare, har na share na hakura saboda na san matukar na fito diban abinci xan iya samun matsala da innah salamatu, har na hakura naji abin ba mai yiwuwa bane matuƙar muka wayi gari a haka zamu iya samun matsala. daurewa nayi na tashi na don samo mana abinda zamu kai bakin salati, ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar korar mu daga gidan gaba daya. A hankali na lallabo na fito daga dakin innata saboda bana so ita kanta tasan zan fita, indai ta sani sai ta dakatar da ni saboda bata son abinda zai bata mata rai. Kasancewar innata mace ce mai saukin kai bata fiye son abinda zai kawo tashin hankali ba, wannan dalilin ya sanya aka mayar da ita bora saboda hakuri da kawar da kai irin nata. Inna salamatu da yayanta su suke juya gidan duk a abinda suke so shi ake yi.
Bakin murhu na nufa a hankali na bude tukunya, tuwo miyar kuka na gani, ba karamin dad'i naji ba saboda rabon da na sanya wani abu a bakina tun abincin safe. tsugunnawa nayi tare da yin bismillah na fara cin tuwon, kafin kace me tuni naci rabinsa, daga nesa na hango ana haskani da fitila a raxane na mike tare da boye hannuna a bayana, sai da ta karaso daf da ni sannan na ga ashe innah salamatu ce, wani kallo ta sakar min wanda ya sanya jikina rawar ɗari, kafin tace min wani abu tuni hawaye sun cika idona, don na san na taro kwai tara tsinana, na janyo wa kaina da innata masifar da Allah ne ya san ƙarshen ta, tsungunawa nayi tare da rokonta ta yafe min