WANI GIDA...!
  • Reads 128,254
  • Votes 12,200
  • Parts 31
  • Reads 128,254
  • Votes 12,200
  • Parts 31
Complete, First published Jan 01, 2020
Tana shiga cikin dakin, taji an janyo hannunta anyi gefe da ita. Cikin tsananin tsoro da bugun zuciya ta daga baki zata saki ihu, taji an sanya hannu an rufe mata baki, a lokaci guda kuma aka juyata tana kallon wanda yayi mata wannan aika-aika. 
Ta saki wani numfashi da bata san lokacin data rike shi ba, ta jefa mishi harara cikin wasa. Duk da cewa manyan fararen idanunta babu abinda suke fitarwa sai tsananin kauna mai tsafta. 

Ya kasheta da murmushin nan nashi da har kullum yake kashe mata jiki, ya kanne mata idanu, 
"Hello, love!".

*

Wai bahaushe yace 'hali zanen dutse!', 'mai hali baya canza halinsa!'. 

Bahijjatu tayi tunanin wadannan duk fada ce kawai, sai da ta kwashe watanni shida bata cikin gidansu ta koma, ta ga babu abinda ya canza zani daga tsarin rayuwar gidan. 

Wata irin rayuwa ce ake yi a cikin gidansu mai matukar daure kai. Rayuwar da babu girmama na gaba, babu bautar Allah, babu kuma tsoron Allah a cikinta. 

Bata san cewa rayuwarta na shirin yin juyi wanda bata taba zata ko tsammani a wannan dawowar ba. 

Ku biyo matashiya Bahijjatu domin jin ta yadda zata karbi wannan canji da yazo mata babu zato balle tsammani, ba kuma tare da ta shirya ba. 

Wannan littafi kyauta ne, wanda zai dinga zo muku a duk lokacin da damar yin typing ta samu... :)
All Rights Reserved
Sign up to add WANI GIDA...! to your library and receive updates
or
#1jeeedorhh
Content Guidelines
You may also like
You may also like
Slide 1 of 10
BAƘAR AYAH cover
တောပန်းလေးမို့ အရိုင်းဆန်သည် ။ cover
SHIN SO DAYA NE? (Complete)  cover
SAREENAH cover
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) cover
UMMI | ✔ cover
RUWAN ZUMA (completed) cover
SHU'UMIN NAMIJI !!    (completed) cover
EX-pect cover
HAFSATU MANGA cover

BAƘAR AYAH

35 parts Complete

..........."Hajiya kar burin ɗaukar fansa ya shiga ranki,ki kasa gane wane irin makami kike son sokawa kanki da kuma danginki. Kawota cikin zuri'arki tabbas zata magancemiki Masifar da kike ciki,saidai kina ƙoƙarin korar macijiyane da wata macijiyar,kina ganin hakanne mafita?"..... ......."Ni bandamu damai zatayi ba,indai har zan daina buɗar ido ina kallon wannan matsiyaciyar a cikin gidana,to komai ma yafaru,ko mai zai faru saina sake ɗaura masa aure da wata,naga shin itama zata kasheta kaman sauran matan,ko kuma wannan zatafi ƙarfinta"...... "Zaro ido tayi ganin tabbas dagaske take abinda ta faɗa,shin hajiyah kuwa wacce irin uwace,bata damu da rayuwar ɗanta ba indai akan cikar burinta ne,hmmm zakuwa tayi maganinki kema,nidai babu ruwana,sojoji ma sunyi sun barta ballantana kuma ke".....ta faɗa a cikin ranta.......... ........Meee amarya tazo da ɗan shege wata biyu?! Sannan kuma a matsayin Budurwa akan Aurota???. "Eh haka ne,dan gatacan ma a falonta tana bashi mama,wai bataga wanda ya isa yasakata tashi tazo gaisheki ba ɗan bai ƙoshi ba"...... "Haka tace".... "Tabbass" Ohh nabaku satar amsa dayawa a cikin littafin Baƙar Ayah,mai son ganin mai zai faru yashigo a dama dashi kawai.......