Tsokaci...........!
Labari ne akan rayuwar wata baiwar Allah me cike da abubuwan al'ajabi, me hade da tashin hankali da jarabawa iri daban daban.
Sanin ita wacece yana da nasaba da fadawarta cikin yanayin data tsinci rayuwarta. Duk da kasancewar bango a gareta ita ce babban silar komai daya faru da ita.
Gararin da mahaifiyarta ta saya a ciki ne ya zamewa rayuwarta bala'i alokacin da taso taci moriyar rayuwar nata.
Sarkakiyar da ta fada ya sata tsanar rayuwa, wanda har tayi soyayya da kanin mijinta ba tare da ta sani ba.
Sai da lokaci ya kure sannan karshen tika tikanta ya zama tik.
*****Labarinnan kirkirarre ne, duk wanda ko wadda hakan yayi yanayi da rayuwarsa/ta tow yayi hakuri hakan baya nufin cin zarafi ga kowa.
*****Taku a kullum Nana Khadija Shuaib, da fatar zaku nishadantu ku kuma ilmantu da abubuwan da labarin ya kunsa.
*****Ga masu san karatun littafan turanci, ana iya duba littafina me suna "COLOURS OF LIFE".