Sai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai.
Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin "Ina za ki tantiriya a cikin wannan daren?". a daidai wannan lokacin gwaggo talatuwa, mai bakin kara, kamar daman jiraye ta ke da taji Kaka ta yi maganar, ta mike zaune tare da gyara daurin dankwalin ta, ta ce, "Ba wai tambayar ki a ke yi ba?"
A takaice na ce "Fitsari zan yi". Banma tsaya jin ta bakin su ba Na kamo hanya ta ta fita daga cikin dakin a hasale, sai da na kawo daf da fuskar Gwaggo Talatuwa sarkin kicihi, da ta gama sakin baki da ido tana kallona cike da fuskar jin haushi, nan take na dade da dubin fuskarta na wanke ta da tukwicin wata kafurar Tusa mai bala'in warin tsiya, a daidai lokacin da na fahimce komai ya tafi daidai kamar yanda nake buk'ata, na bar dakin a hanzarce tare da daukar wata waka ta Ado Gwanja a baki, ina tafe ina raira abita kamar daman ni nayita, na barsu dwade da hanci dan babu bakin yin magana......
FOLLOW
VOTE
COMMENTS
AND
SHARE
"THANKs."