Jiddah yarinya ce 'yar kimanin shekaru 16 wadda take wahalar rayuwa ta kula da kanta da mari'kiyarta, wani 'karamin al'amari ya faru wanda ya sauya rayuwarta gaba d'aya saidai ya sabuwar rayuwar jiddah zata kasance? INA GATANTA a lokacin da aka bi son zuciya aka turata wannan halaka? Shin a yanzu xata samu wannan GATA da take muradi na tsawon rayuwarta? Waye zai zama GATANTA a wanna lokacin da danginta da mahaifinta ke gudunta tamkar ta aikata abin kunya bayan batada ko d'igon laifi?
Yaya Sulaiman zaiyi da wutar soyayyar Jiddah dame huruwa a cikin ransa bayan abinda ya aikata wanda har danginsa sukayi tir da wannan dabiar tasa? Yayi anfani da GATAN da yake da wajen neman tarwatsa mata rayuwa saidai shi INA GATANSA a wannan lokaci da yake neman jiddah ido rufe, bayan yayi amfani da RASHIN GATAN TA ya cutar da rayuwarta.