Huda kyakyawar yarinya ce son kowa kin wanda ya rasa. Amma iyayen ta sun kasance talakawa gaba da baya. Ta taso cikin wuya da kuncin rayuwa.
Rasuwar mahaifinta yasa ta kuduri niyar samun kudi ko ta halin yaya ne. Bata abota da kowa sai masu shi. Ta dauki sona abun duniya ta daura wa kanta.
Amma son mutum daya data kamu dashi zai iya barinta ta cimma burinta?
Wanan labarin yana dauke ta tarin soyayya, cin amana, yaudara da kuma irin halin da yan mata masu son abun duniya suke jefa kansu ciki.💔