Rayuwa na cike da ƙalubale kala kala. Allah na jarabtar bayinSa a duk yanda Ya so, hakan ba yana nufin ba Ya son su ba. Kyawun halitta, tarin dukiya ko mulki ba shi ke nuna son Allah akan bawanSa ba. Amma dayawa mutane kan manta haka.
Me yasa suke ganin laifin ta akan abunda su da ita basu da iko akai? Me yasa suke ƙasƙantar da ita suke wulaƙanta ta da ahalinta akan abunda Allah Ya azurta su da shi? Wanda ba dubarar su ko wayon su ya saman musu ba, hakan kuma baya na nufin sun fi su wajen Allah ko sunfi su kusanci da Shi ba.
Ba'a cire rai da rahamar Ubangiji, dan haka Maimoon bata fidda rai ba. Wataran zasu fita daga mawuyacin halin da suka tsinci kan su ciki, zasu samu kwanciyar hankali da farin ciki mai ɗaurewa.
Amma faruwan wani al'amari yasa Maimoon tantama, anya suna da rabo anan duniyan? Musamman ma ita.
***
Idanunta kaɗai ya gani duniyar shi ta juya gaba ɗaya. Allah Ya yi halitta a wurin! Bai taɓa ganin idanu masu kyau haka ba, gasu farare kal! Kaman farin wata. Amma kuma a maimakon ya gano haske kaman na wata sai ya gano duhu mai rikitarwa, duhun da ya hango cikinsu ya tada mai hankali. Tabbas ba zai samu sukuni ba har sai yaji labarin rayuwarta kuma har sai haske ya mamaye duhun da ya gani.
© Wannan littafin mallakar Maimunatu Isyaka Bukar ne. Duk haƙƙoƙi. Babu wani ɓangare na wannan takaddar da za a sake fitarwa ko watsawa ta kowace hanya, lantarki, inji, kwafin hoto, rakodi ko wani abu ba tare da rubutaccen izinin Maimunatu I Bukar ba.
Wannan aikin almara ne. Sunaye, haruffa, kasuwanci, wurare, yankuna, da abubuwan da suka faru ko dai samfuran marubucin ne ko kuma anyi amfani da su ta hanyar ƙirƙirarrun labarai. Duk wani kamanceceniya da mutane na ainihi, rayayyu ko matattu, ko kuma ainihin al'amuran sun faru ne kawai.
©Maimunatu I BukarAll Rights Reserved