#10 Hausanovel, 15 June 2020.
#47 Nigeria june 2021.
Duniya Labari,
Duniya Makaranta,
Duniya Kasuwa,
Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa kafa su rusa.
Ta rasa me ɗaya zata yi taji sassauci a halin da take ciki, a ɓangare guda kuma ta rasa da wane ɗaya zata ji cikin abubuwa barkatai da sukai mata katutu a cikin wannan duhun dare, shin za taji da halin baro innarta da tayi cikin mawuyacin halin da bata da gata sai Allah? Ko da mutuwar Baba zata ji? Ko za taji da dabi'ar ƴan gidan su ne? Ko ko za taji da hanyar gidan su Naty data ɗinke mata ne? ta jefa ta tsundum cikin wata duniya sabuwa da bata san kowa da komai game da ita ba? Shin ita Bintu wai dama haka rayuwar take da tarin ɗaci da maƙaƙi a wuya? Haka duniyar take da kwazazzabe da tarin ramuka a cikinta? Nan ta ƙara sautin kukanta tana darzar majina.
***
Garin yayi tsit baka jin komai sai kukayen tsuntsyen da suke ma Bintu rakiyar da bama tasan da shawagin su ba. Iskar dake ta kaɗa yaloluwar doguwar rigar dake jikinta yana wasa da jelar shukun kanta ma bata san da zaman shi ba, domin duk wasa sensory receptors da neurotransmitters dama duk wasu jijiyoyi dake aikin kai ma ƙwaƙwalwarta rahotanni. Sun tsaya cak sun tafi hutun taƙaitaccen lokaci.
***
Tayi tafiya mai tsawo! ita kanta bata san adadin tsowon data ɗauka tana tafiya cikin babin ƙaddarar rayuwarta ba, take kuma aka maido nepa a cikin ƙwaƙwalwarta, tsayawa tayi cak ta dubi gabas da yanma, kudu da arewa amman ba hanyar da tai mata tayin sani.