Aƙida kan iya zama linzami akan tafarki na Rayuwar Ɗan Adam Aƙida kan iya zama linzami da zai ja kansa da kansa ?? ( yayi jagora a fagen tafiyar rayuwar Ɗan Adam ) . Ba koyaushe Ɗan Adam yake da zaɓi ba akan aƙidar sa . A hankali aƙida take sanɗar Ɗan Adam har ta shiga ta saje da halayyarsa da kafin ya farga tayi masa rumfar da ba shi da zaɓi wajen irin yanayin da zata iya zo masa da shi . Amma me zai faru a lokacin da aƙidar ta zurfafa har ta kai mai ita ga makancewa daga ganin zuzzurfan ramin da ya mamaye kan tafarkin aƙidar sa ?? Ya kuma gaza wajen riƙo linzamin akiɗarsa maimakon haka sai ya sakar mata linzami har ta kai maƙuryar ƙurewar da ta birkice ta jirkita ta rikiɗe ta koma mummunar akiɗar da ta zama guba sannan kuma annoba acikin al'umma sannan ta jefa mai ita a hallaka mafi munin ji da gani . Anya Salman bai yi fargar daji ba ? Lokacin da ya farga ya fara yunƙurin riƙo linzamin aƙiɗarsa ya dawo da ita bisa kyakkyawan tafarkin da ainahi ya gina akiɗar zuciyar sa a kai , a kuma dai-dai lokacin ne zuciyarsa tayi masa tirjiya ta jaa ta toge sakamakon aƙidarsa da tayi arangama da wata aƙidar da take mabambanciya da ta shi . So kuma yayi tasiri irin nasa ta hanyar sarƙe tsakanin aƙidun biyu da suke kishiyoyin juna ba tare da ya lura da tazarar da ke tsakanin su ba . Sannan a ƙarshe zuciyoyin su suka zaɓi da suyi watsi da tasirin aƙidunsu su rungumi junan su a tsakiyar bigiren da ko cikin shuɗaɗɗun mafarkai irin na baccin tsakiyar hunturu , ɗayan su bai taɓa tsintar kansa a ciki ba sai ga rayuwa ta juya musu aƙida kuma ta musu jagora . Shin wai gaske ne aƙiɗar ka linzamin ka ??? Sahihiyar amsar tana ga Salman tare da Madinah .All Rights Reserved