Za ku ji cewa littafi ya ƙunshi labaru na soyayya, jarumta da abubuwa iri daban-daban waɗanda su ka damganci sha'ani na bokanci da kuma tsafe-tsafe. Za kuma a ji cewa wannan littafi ya shafi ɓangaren addini da sauran mu'amuloli na rayuwar duniya, don haka waɗannan labaran da aka bayar za su iya zama ƙirƙirarru ko kuma su zamto sun taɓa aukuwa a haƙiƙa.