Mafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga cikinmu kyau shine abin so , komi mai kyau mukeso ba ruwan mu da badinin abin, tuhume tuhume sunyi yawa kan ya'yan masu kudi, da dama ana ganin basu iya komi ba! Daga kan darajta dan adam, tsoron Allah su, zaman aurensu da mu'amalarsu da tarbiyarsu, ko kunsan dan talaka yafi Dan maikudi iya izza da wulakanta dan adam idan ya samu ko duniya a hannunsa, ba duk abinda ka gani bane yake zama dai dai da ko tunaninka.
Dayawanmu ZABIN ALLAH bashi bane abinda mukeso, mukanso ra'ayin zuciya da abinda ta kullah, har ya kaimu ga ZABEN TUMUN DARE! Zabi mafi muni a rayuwa..........
Ku biyoni dn jin yadda ZABIN MUHAMMAD KABEER yake kasancewa cikin duniyar tunaninsa.