***Wannan labarin somin tabi ne. Za a iya samun cikakken labarin akan manhajar Okada cikin watan Janairu, 2021. In sha Allah***
***
#1 aure 9th 01 2021
Tarihi yana kunshe da fuskoki da dama. Banda na wucewar abunda ya shude harda kasantuwar abunda ya shude a rayuwarmu ta yanzu. Sannan a duk lokacin da aka Maimaita tarihi, farashin yana karuwa ne fiye da kima.
Hakan ne ya faru da Maryama-Siddiqa a lokacin da ta dauki alwashin bazata bari ta maimaita tarihi ba duk da kasancewa dukkan alamu sun nuna hakan ne yake shirin faruwa.
Bayan zaman aure na tsawon shekaru ashirin tare da mijinta Sufyaan Barkindo Sajoh, sun gamu da kalubale wanda ya sa Sufyaan tono abunda ya dade da burnewa yayinda Siddiqah ta jajirce wurin neman 'yancinta daga rayuwar da ta samu kanta a ciki.
Sai dai komai ya kwabe musu a lokacin da suka samu masu kalubalantar matakin da suka dauka. Siddiqa ta gamu da abokan hamayyar da suke neman rayuwarta wadanda bazasu tsaya ba har sai sun ga karshenta.
Shin zata zakulo kanta daga wannan kangin, ta samu rayuwar da ta yi karfin halin mafarki wa kanta, ko kuwa za a maimaita tarihi ne?
Shin wani bangare Sufyan zai zaba idan tura ta kai bango?
***