16 parts Complete Rayuwa mai ɗauke da ƙunci da kuma tarin baƙin ciki, Yayinda hasken wata ke fitowa yana haskaka samaniya, a lokacin ne kuma zuciya keyin zafi da wani irin tafarfasa, Idaniya sun makance dalilin zubar Hawayen da ban san yaushe ne zai tsaya ba, Ina jin inama zan iya kashe kai na! Ko hakan zai sanya zuciyata ta samu nutsuwa da kuma salama, a lokacin da kowa ya kamata yayi farin ciki a lokacin na kejin duniya nayi min zafi, Idaniyan zuciyata na tafarfasa, ban sani ko zan zama dai-dai kamar kowa? Ban san yaushe rayuwa zata juya min daga juyin wainar fulawan da take dani ba, rayuwata ita ake kira da GABA GAƊI rayuwa mara ƴan ci, ko wacce mace na amsa sunanta dana mahaifinta yayinda ya kasance ni kuma ina amsa sunana kana na bashi makari da TSINTACCIYA!