Ahmed ka manta Wacece ni...? Nice fa masoyiyarka Samiha..? ka manta alƙawarinmu...? Ka manta yadda muka tashi muna gina yadda rayuwar Aurenmu zata kasance..? amma yau rana ɗaya saboda wani dalilinka mara tushe ballantana makama kakeso kaƙi amfani da damar data samemu Ahmed...?" hannu ya ɗaga mata lokaci ɗaya yana faɗin "Ya isa haka Samiha..! Nace ya isa haka...? Ya kikeso nayi dake ne eh..? karki manta ke matar Aure ce yanzu duk waɗannan burukan namu sun yanke daga lokacin da mahaifinki ya bada ke..! taya ya zan iya bin buƙatarki alhalin kina matsayin matar Uban gidana..! kuma nima ina matsayin surukinsa ina auren 'yarsa ta cikinsa kuma sai na biye miki naci amanarshi..? A'a ba zai taɓa faruwa ba bazan taɓa yima megidana haka ba SILAR HALLACIN dayayi min bazai taɓa barina na iya cin amanarsa ba SAMIHA... Kiyi Haƙuri...! Watch Out In....SILAR HALLACI...