Duk kansu suna da buri tare da boyayyen sirri a zuciyarsu, zanen kaddara kan iya fadawa ko wani mutum sai dai wasu suke kirkirar kaddarar, su zanata da kansu ba tare da sunyi la'akari da tunanin abinda zai je ya dawo ba. Tsantsar damuwa, tashin hankali, soyayya, zalunci, zamantakewar aure, rashin lafiya, sata, makirci, zina, cin amana, kishi, kazafi duk suna cikin wannan tafiya mai cike da rudani. Aka ce ranar wanka ba'a boyon cibi kamar yadda zai kasance karshen alewa ƙasa.